Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ya Yabawa Shugaba Buhari
Abin mamaki a cewar wasu, shugaban jam’iyyar adawa ya yabawa shugaba Buhari
Secondus ya jinjinawa Buhari saboda ya ajiye siyasa gefe wajen zaben Okonjo-Iweala – Tsohuwar ministar kudi na Najeriya na gab da zama mace ta faro da zata zama shugabar kungiyar kasuwancin duniya Jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) ta jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da ya nunawa Dr Ngozi Okonjo Iweala a takaran da take yi na shugabancin kungiyar kasuwancin duniya WTO.
Read Also:
Shugaban uwar jam’iyyar, Uche Secondus, yayi wannan jinjinawan a jawabin da mai magana da yawunsa, Mr Ike Abonyi, ya saki ranar Laraba, Vanguard ta ruwaito. Secondus ya ce Najeriya za ta kafa tarihi idan Okonjo-Iweala ta zama mace ta farko a duniya da zata zama shugabar kungiyar WTO.
Ya yabawa shugaban Buhari kan ajiye siyasa gefe da yayi wajen goyawa Okonjo-Iweala baya da kuma Dr Akinwumi Adesina, shugaban bankin cigaban Afrika (AfDB) bayan da yayi har suka samu nasara. Ya ce nasarar Okonjo Iweala na zuwa ne bayan tazarcen Adesina matsayin shugaban bankin AfDB, kuma hakan ya farantawa PDP rai saboda dukkan wadannan mutane biyu tsaffin Ministoci ne a gwamnatin PDP.