Kungiyar PTF ta Koka da Karuwar Cutar Korona

 

Kwamitin PTF ya zargi kungiyoyin addini da laifi wajen yaduwar COVID-19.

A halin yanzu cutar ta sake dawo wa, ta na harbin mutane a jihohin Najeriya.

Boss Mustapha ya ce ana saba ka’ida wajen kiran taron addini, ana cincirindo.

Kwamitin PTF mai yaki da annobar COVID-19 a Najeriya ya zargi wasu kungiyoyin addini da saba dokoki da sharudodin da aka gindaya a kasar.

PTF ya yi wannan magana ne bayan an fara samun karuwar masu dauke da cutar a cikin ‘yan kwanakin nan, inda lamarin ya yi kamari sosai.

Da yake jawabi a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, 2020, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya zargi malamai.

Mista Boss Mustapha ya shaida wa ‘yan addini cewa kungiyoyin addini sun rika kawo cikas ta hanyar tara jama’a ba tare da la’akari da ka’idoji ba.

Mustapha ya yi wa manema labarai yadda annobar ta yi tasiri a al’umma ta hanyar jawo rikici, tabarbarewar lafiyar kwakwalwa da shan kwayoyi.

Boss Mustapha yace PTF na aiki da masu fada a ji da masu ruwa da tsaki domin ganin an shawo kan wadanna matsaloli da ake fuskanta dalilin annobar.

Jaridar The Nation ta rahoto SGF ya na cewa: “Mun lura cewa, abin takaici, ‘yan Najeriya, musamman kungiyoyin addini, sun cigaba da shirya manyan taro da ke iya yada cutar.”

“PTF ta na kira ga duk kungiyoyin kasa cewa babban nauyi ne a kansu su tabbatar an bi doka da sharudan da aka gindaya domin hana yaduwar cutar.” Inji Mustapha.

Yayin da ta ke shirin gabatar wa shugaban kasa rahoton karshe, PTF ta gargadi jama’a game da cinkoso lokacin biken kirismeti da bikin sabuwar shekara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here