Qatar ta Magantu Kan Yaƙin Amurka da Iran

 

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar, ta ce ƙasar ba za ta shiga aikin sasanta tsakanin Amurka da Iran ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran ba.

Kakakin ma’aikatar Majid Ansari ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar a Doha, babban buirnin ƙasar.

Mista Ansari ya ce a yanzu abin da ke gaban Qatar shi ne kawo ƙarshen hare-haren da ake kai mata na kare kai.

A shekarun da suka gabata, musamman kafin yaƙin kwana 12, Qatar ta kasance ɗaya daga cikin masu shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran.

da aka tambaye shi Qatar za ta ci gaba da hukɗa da Jamhuriyar Musulunci bayan hare-hare kan ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Gulf, sai Ansari ya ce ”E za mu ci gaba ai ba za mu iya raba kanmu da juna ba”.

Ya kuma ce Qatar na tattaunawa daa Amurka don lalubo hanyoyin diplomasiyya.

”Gwamnatin Amurka ta yanke shawara fara wannan yaƙi ne saboda fargabar da take da shi kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya”, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa Qatar na aiki da Amurka don yayyafa wa yaƙin ruwa da dakatar da hare-hare ”kan ƙasashenmu”.

Ya zuwa yanzu ƙasashen Masar da Pakistan da Turkiyya na ƙoƙarin shiga tsakani don kawo ƙarshen yaƙin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here