Gwamnatin Tarayya za ta Raba Keke Napep 2000 Mai Amfani da Gas

 

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta ce an kammala shirin raba baburin adaidata sahu mai amfani da iskar gas na CNG ga matasan kasar nan 2,000.

Rabon da za a yi shi ta ma’aikatar cigaban matasa ta ce rabon wani bangare ne na bikin cikar Najeriya 64 da samun yancin mulkin kai.

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa karamin Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawale ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai a ranar Juma’a.

Gwamnati za ta raba adaidaita sahu ga matasa

Karamin Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawale ya ce raba babaran masu kafa uku da ke amfani da iskar gas samfurin CNG zai taimaki sana’ar matasa.

Ya ce matasan da za su rabauta da baburan za su rika kashe 20% na abun da su ke kashewa kan fetur a halin yanzu.

Gwamnati za ta cigaba da tallafawa matasa

Gwamnatin tarayya ta ce za matasa 2,000 da za a ba babura masu kafa uku su ne kashi na farko a cikin shirin raba abin hawan don gudunar da sana’a.

Mista Ayodele Olawale ya bayyana cewa ana sa ran masu amfani da baburan za su samu karuwar riba, da rage tsadar sufuri ga fasinjojinsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here