Yadda Aka Raba Mukaman Shugabancin ADC a Jihar Kano
Kano – Ƙungiyar Kwankwasiyya a cikin jam’iyyar ADC ta amince da karɓar kashi 30 cikin ɗari na mukaman shugabanci a Kano.
Hakan ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin ɓangarori daban-daban da ke a jihar Kano.
Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ta cimma yarjejeniya da ɓangaren Atiku Abubakar da kuma na Nasiru Yusuf Gawuna, cewar The Guardian.
Yadda aka tsara mukaman ADC a Kano
Dukkanin Kwankwaso da Gawuna sun fice daga jam’iyyunsu na baya, inda suka koma ADC domin sake tsara siyasar su da ƙoƙarin karɓe iko daga jam’iyya mai mulki a Kano.
Kwankwaso ya sake duba dabarunsa na siyasa domin ci gaba da riƙe tasirinsa a Kano, bayan ya rasa ikon tsarin da ya samar da gwamna Abba Kabir Yusuf.
A ƙarshe, ɓangaren Atiku Abubakar ya samu kashi 40 cikin ɗari na mukaman shugabanci, yayin da na Gawuna da Kwankwasiyya suka samu kashi 30 cikin ɗari kowanne.
Martanin jam’iyyar ADC a Kano
Read Also:
Mai magana da yawun jam’iyyar na riƙo, Sa’id Bello, ya ce wannan tsari zai taimaka wajen haɗa kan dukkan ɓangarorin jam’iyyar a Kano.
Bello ya bayyana cewa tsarin rabon mukaman zai shafi matakai daga ƙananan hukumomi har zuwa jiha, domin tabbatar da adalci da wakilci ga kowa.
Ya ƙara da cewa:
“Ƙungiyar Kwankwasiyya za ta riƙe kashi 30 cikin ɗari, yayin da tsohon tsarin ADC na hannun mabiyan Atiku zai riƙe kashi 40 cikin ɗari”.
Ya kuma ce ɓangaren da ke biyayya ga Nasiru Yusuf Gawuna zai samu kashi 30 cikin ɗari na mukaman shugabanci a jam’iyyar, cewar Tribune.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa ciki har da Kwankwaso, Aminu Abdussalam, Akilu Indabawa, Nasiru Gawuna, da Sanata Rufa’i Sani Hanga.
Sanata Lawal Adamu Usman ne ya jagoranci taron, inda aka ba shi alhakin tabbatar da haɗin kai tsakanin ɓangarorin jam’iyyar ADC a Kano.
An gudanar da taron a gidan Kwankwaso a Kano, inda aka tattauna hanyoyin da za su tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
Jigon ADC ya tattauna da Legit Hausa
Wani jigo a ADC daga jihar Kano ya fadawa wakilin Legit Hausa halin da ake ciki game da tsara yadda rabon makaman zai kasance.
Hon. Adnan Tudunwada ya ce tuni aka sauke su inda ya nuna waɗanda aka nada a wata takarda da ya yada.















