Mutane 10 Sun Rasa Rayukansu a Hare-Haren Sama a Gaza
Akalla mutane goma ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare ta sama da Isra’ila ta kaddamar cikin dare a Zirin Gaza.
Sojojin Isra’ilar sun ce sun hari mambobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ce ta Islamic Jihad.
Read Also:
Fararen hula na daga cikin wadanda suka mutu, yayin da aka kaddamar da hare-haren ta sama wadanda suka fada kan Gaza da kuma Rafa lamarin da ya jefa tsoro a zukatan mazauna biranen.
Hukumomin Falasdinu sun tabbatar da mutuwar mutane goma da kuma wasu da suka samu raunuka wadanda ba’a tantance yawansu ba.
A sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce wasu manyan kwamandojin Al-Qudus Brigades wato reshenta na soji uku sun yi shahada a hare-haren.