Rasha na Ci gaba da Kai Hare-Hare Birnin Bakhmut na Ukraine

 

Jami’ai a birnin Kyiv, sun ce Rasha ta zafafa kai hare-hare da makaman Atilari da na roka a kusa da birnin Bakhmut na Ukraine.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai sama da hare-hare 300 cikin kwana guda, amma bayanai sun ce dakarun Rasha ba su yi nasarar sake dannawa wasu kauyuka biyu da ke yankin ba.

An kuma kai wasu hare-haren a arewacin birnin kusa da Kupiansk.

Jami’an Ukraine sun tabbatar da mutuwar mutum guda, lokacin da makami mai linzamin da Rasha ta harba ya faɗa gidajen jama’a a kudancin birnin Mykolaiv.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here