Leƙen Asiri: Rasha ta Kama Mutune 25 

 

Jami’an tsaron Rasha sun ce sun kama mutum 25 a yankunan kudancin Ukraine da Rasha ta mamaye.

Sun ce sun kama mutanen ne bisa zargin cewa suna taimakawa Ukraine ko kuma yi mata leƙen asiri.

Jami’an tsaron sun ɗauki mutanen ne a yankunan Kherson da Zaporizhzhia inda kuma ake yi wa mutanen zargin cin amanar ƙasa.

Tun a farkon shekarar nan, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Alla-wadai da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here