Black Friday: Rashin Abinda Fada – Shehu sani ga Kano Hisbah

 

Hukumar Hisbah ta Kano na cigaba da shan suka daga bangarori daban-daban.

Bayan sabanin da ta samu da malaman Kano, Sanata Shehi Sani ya yi martani.

Tsohon Sanata da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki hukumar Hisbah ta jihar Kano kan gargadin da ta yiwa gidan rediyo na amfani da kalman ‘Black Friday.’

Sanaya a shafinsa na Tuwita ya ce wannan rashin aikin yi ne kuma yayi kira ga Hisbah ta mayar da hankalinta kan garkuwa da mutane da kashe-kashen da ake yi a Arewa.

“Ranar Juma’a babbar rana ce ga Musulmai. Dan an ambaceta da wani kala ba wani abu bane. Barazabar Hisbah kan amfani da kalmar ‘Black Friday’ aikin banza ne,” cewar Shehu Sani.

“Su mayar da hankali kan kashe-kashe da sace-sacen mutane a garinsu. Ana bukatansu a filin daga,” ya kara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here