Gwamnonin Kudu Maso Gabas Sun Nuna Rashin Goyan Bayan Su Akan Kungiyar IPOB

 

Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas janye kanta daga kungiyoyin da ke neman ballewa a yankinsu.

Hakazalika gwamnonin sun yi Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan kiraye-kirayen wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Sun bukaci Najeriya ta ci gaba a matsayin tsintsiya madaurinta daya.

Membobin Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas sun nesanta kansu daga kungiyoyin da ke kira ga ballewa a yankin da sauran sassan kasar.

Sun kuma yi Allah wadai da rikice-rikicen da suka biyo bayan tashin hankalin wanda ya kai ga asarar rayuka da asarar dukiyoyi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnonin sun hadu ne a ranar Asabar, 19 ga watan Yuni, a jahar Enugu domin tattaunawa kan hanyoyin magance matsalolin tsaro da maido da zaman lafiya a yankin.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, ya yi magana a madadin gwamnonin a karshen taron inda yace:

“Mun yi tir da duka ayyukan kungiyoyin masu neman ballewa a Kudu maso Gabas da sauran wurare.

“Mun tabbatar da cewa ba ma goyon bayansu, ba da yawun Kudu maso Gabas suke magana ba.

“Tunanin cewa shugabannin Kudu maso Gabas sun yi shiru a kan neman ballewar wasu daga cikin matasanmu ba daidai ba ne.

“Gwamnonin Kudu maso Gabas, Shugaban Ohanaeze, mambobin Majalisar Tarayya, mashahuran shugabanni sun fito fili a lokuta da dama a baya don yin magana game da irin wannan hargitsi.

“Don kar a lalata halin da ake ciki mara dadi, shugabannin Kudu maso Gabas sun kafa wani kwamiti da zai tattauna da irin wadannan matasa don su tsaya su bar dattawa su yi magana don magance irin wannan fargaba.”

Sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da ayyukansu a bisa ka’idojin aiki da doka. Sun kuma bukaci mambobin majalisar kasa daga yankin Kudu maso Gabas da su goyi bayan kirkirar ‘yan sanda na jahohi a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ke gudana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here