Rashin Iyan Zazzau da Talban Zazzau: Shugaba Buhari ya Mika Sakon Ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Kaduna
Mutuwar manyan jiga-jigan masarautar Zazzau biyu ya ja hankalin Shugaba Buhari.
Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa Buhari bai ji dadin afkuwar abun bakin cikin ba.
Buhari ya aika sakoon ta’aziyya ga mutanen Kaduna a kan lamarin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki a kan mutuwar manyan jagorori biyu a Masarautar Zazzau, Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu da Talban Zazzau, Abubakar Pate a rana daya.
Read Also:
A sakon ta’aziyya da babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya saki a ranar Juma’a a Abuja, Buhari ya bayyana mutuwarsu a matsayin abun bakin ciki biyu.
Ya ce:
“Mutuwar wadannan manyan jiga-jigai biyu a masarautar Zazzau ya zo mani da kadawar zuciya saboda ba a jima ba da rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
“Ina mika jajena ga iyalan mamatan biyu, masarautar Zazzau, masarautar Zazzau, gwamnati da mutanen jihar Kaduna.
“Allah Ya gafarta musu, Ya karbi kyawawan ayyukansu, Ya sanya su cikin Aljanna.” A halin da ake ciki, Shehu ya ce Shugaban kasar ya tura tawaga zuwa Fadar Sarkin Zazzau don gabatar da ta’aziyya a madadinsa, jaridar The Guardian ta ruwaito.