Rashin Tsaro Ya ci Tura – Sarkin Musulmai

 

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar II, ya yi Alla-wadai da lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya, inda yace yan bindiga na cin karansu ba babbaka.

Sarkin Musulmi wanda shine shugaban majalisar koli ta lamuran addini a Najeriya ya bayyana cewa yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna awon gaba da mutane a Arewa.

Alhaji Sa’ad ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin taron majalisar hadin kan addinai NIREC da akayi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sultan yace: “Yanzu nawa albasa a kasuwa a Najeriya, wannan zai fada maka irin halin kakanikayen da ake ciki a kasar.”

“Ba wai babu shawari bane ko babu yadda za’a magance matsalolin ba. Kawai abinda muka rasa shine rashin niyya.”

Karin bayani na nan tafe….

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here