Za ku Iya Rayuwa Mai Amfani a Sabuwar Shekara – Jonathan ga ‘Yan Najeriya

Goodlucck Jonathan ya bayar da bayanai kan yadda yan Najeriya za su iya rayuwa mai amfani a sabuwar shekara.

Tsohon shugaban kasar ya gano wasu koma baya da suka afku a kasar a 2020.

Jonathan ya bayyana dalilin da yasa bai kamata al’umman kasar su bari matsalolin baya ya shafi makomarsu na gaba ba.

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci al’umman kasar da su koyi darasi daga matsaloli, riba da rashin da aka yi a shekarar 2020.

Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu, a sakonsa na sabuwar shekara zuwa ga yan Najeriya ta shafin Twitter.

Tsohon Shugaban kasar ya ce 2020 ta kasance shekara mai tattare da kalubale ga gidaje da iyalai da dama saboda annobar korona.

Ya ce baya ga annobar, Najeriya ta kuma yi fama da zanga-zangar EndSARS da tabarbarewar al’ada, tattalin arziki, harkoki da rayuwa al’umma.

Jonathan ya bayyana cewa duk da koma bayan, ya kamata yan Najeriya su koyi darasi daga matsalolin baya.

Ya shawarci al’umman kasar da su ba da muhimmanci ga halayyar da ke nuni ga adalci da zaman lafiya a tsarin Najeriya.

Jonathan ya yaba ma dukkanin yan Najeriya a kan karfin gwiwar da suka nuna a yayinda ake tsaka da fama da matsaloli.

Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa masoyansu sakamakon korona da sauran cututtuka da matsaloli a shekarar 2020.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here