Ƴan Wasan Real Madrid da za su Kara da Alaves a La Liga

 

Real Madrid za ta karɓi bakuncin Deportivo Alaves a wasan mako na bakwai a La Liga da za su kara a Santiago Bernabéu ranar Talata.

Real tana makaki na biyu a kan teburin La Liga da maki 14, bayan cin wasa hudu da canjaras biyu.

Ita kuwa Alaves maki 10 ne da ita a mataki na bakwai, bayan nasara a karawa uku da canjaras daya aka doke ta fafatawa biyu.

Sun kara a bara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, inda Real Madrid ta je ta ci Alaves 1-0 ranar Alhamis 21 ga watan Disambar 2023.

A wasa na biyu kuwa a Bernabeu, Real ta yi nasara 5-0 a kan Alaves ranar Talata 14 ga watan Mayun 2024.

Ranar Juma;a 20 ga watan Satumba Alaves ta doke Sevilla 2-1 a wasan mako na shida, ita kuwa Real ta yi nasara a kan Espanyol 4-1 ranar Asabar 21 ga watan Satumba.

Tuni kociya, Carlo Ancelotti ya bayyana ƴan wasan da Real Madrid za ta kara da Alaves a Bernabeu.

Ƴan Real Madrid da za su kara da Alaves:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.

Masu tsare baya Militão, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, Mendy, Jacobo da kuma David Jiménez.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni da kuma Arda Güler.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo da kuma Endrick.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here