Ribar da Dangote da BUA ke Samu a Cikin Sa’o’i 8
Biloniyoyin Najeriya, Aliko Dangote da Rabiu Abdulsamad, su na cigaba da samun shuhura tare da tumbatsar dukiya ta kasuwancin siminti da abinci.
 Arzikin Dangote ya karu da kashi 0.03 yayin da Abdulsamad BUA arzikinsa ya karu kashi 1.62 wanda ya kai ribarsu N28.85 biliyan and N1.64 biliyan.
 Mamallakin kamfanin siminti na Dangote yanzu haka arzikinsa ya kai $13.4 biliyan, na BUA kuwa ya kai $4.3 biliyan a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba.
Aliko Dangote, mamallakin kamfanonin Dangote da Rabiu Abdulsamad, shugaban kamfanin BUA, sun samu ribar tsabar kudi jimilla N30.4 biliyan a cikin sa’o’i 8.
 Mashahuran masu arzikin sun samu wannan karin kan dukiyarsu ne a kasuwancin ranar Talata.
Yayin da Dangote har yanzu ya fi kowa arziki a Afrika, mai kamfanin simintin bai kai Abdulsamad Bua samun gagarumar riba ba a ranar Talatan inda dukiyoyinsu suka karu da kashi 0.03 da kuma kashi 1.62 daya bayan daya.
Arzikin mai kamfanin simintin Dangoten ya karu inda ya kai $13.4 biliyan inda ya cigaba da zama mutum mafi arziki a Najeriya da Afrika.
Kamar yadda kiyasin da ke bibiyar biloniyoyi na Reuters ya bayyana, ya samu karin N1.64 biliyan cikin sa’o’i takwas kacal.
Arzikin Abdulsamad BUA kuwa a daya bangaren ya karu da kashi 1.62 wanda ya kai jimillar dukiyarsa zuwa $4.3 biliyan bayan ya samu karin zunzurutun kudi har N28.85 cikin sa’o’i takwas kamar yadda kiyasin biloniyoyi ya bayyana.
 A yayin da dukiyarsa ta kai $13.4 biliyan a ranar Talata, Dagote ya zama mutum na 191 a jerin biloniyoyin duniya, yayin da Abdulsamad ya hau mataki na 574.
 Mu sani cewa, Dangote da Abdulsamad suna gasa a masana’antu iri daya insa suke sarrafa siminti, sikari da gishiri. Biloniyoyin 2 a halin yanzu su na hangen masana’antar man fetur ne.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here