Rijistar Layin Waya ba Bisa ƙa’ida ba: Hukumar Dake Kula da Kamfanonin Sadarwa(NCC) ta Kama Mutane 5 a Abuja

 

NCC ta sanar da kama mutane biyar waɗanda take zargi da aikata laifin rijistar layin waya ba bisa ƙa’ida ba a Abuja.

Hukumar ta samu wannan nasara ne tare da haɗin gwuiwar jami’an tsaron DSS, da kuma na hukumar NSCDC.

NCC tace wannan somin taɓi ne, za’a cigaba da gudanar da wannan aikin a sauran jahohin ƙasar nan.

Hukumar dake kula da kamfanonin sadarwa NCC ta sanar da kama wasu mutane biyar da zargin yin rijistar layin waya ba bisa ƙa’ida ba da kuma siyar dashi.

NCC tace an kama mutanen ne a wani aikin haɗin gwuiwa tsakanin sashin saka idanu na NCC, DSS, da kuma jami’an tsaro na NSCDC a unguwar Wuse, Abuja.

Hukumar NCC ta bayyana hakane a wani jawabi da ta fitar a Abuja ranar Alhamis ta bakin Daraktan yaɗa labaranta, Ikechukwu Adinde.

A jawabin yace:

“An miƙa waɗanda aka kama ɗin ga hukumar NSCDC reshen Abuja, domin su ƙara gudanar da bincike kan zargin da ake musu.”

Shugaban sashin ayyuka na NCC, Salisu Abdu, wanda ya jagoranci tawagar haɗin gwuiwar, yace wannan aikin na daga cikin ayyukan da hukumar ta fara na yau da kullum domin daƙile masu laifi waɗanda ake haɗa hannu dasu wajen yin rijistar layi ba bisa ƙa’ida ba.

Salisu yace:

“Yin rijistar layi ba tare da ɗaukar bayanan wanda zaiyi amfani dashi ba babban laifine da ake hukunci kansa ƙarƙashin dokokin kamfanonin sadarwa, hakanan laifine a ƙarƙashin dokokin ƙasa.”

“Duk da gwamnatin tarayya ta ɗage dokar hana yin rijistar sabon layi, ya zama wajibi muyi rijistar sabon layin waya yadda yakamata, kuma mu haɗa shi da lambar katin ɗan ƙasa (NIN).”

Salisu Abdu ya gargaɗi duk wanda yasan yana makamancin irin wannan laifin da ya gaggauta bari tun kafin NCC ta iso gareshi.

Ya kuma tabbatar da cewa wannan aikin zai cigaba a Abuja da sauran jahohin ƙasar nan kamar yadda Punch ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here