Muzaharar Ashura: Rikici ya Barke Tsakanin ‘Yan Shi’a da ‘Yan Sanda a Jahar Sokoto

 

Rikici ya barke yayin taron muzaharar Ashura a jahar.

Sokoto Yan Shi’a sun yi ikirarin cewa an kashe musu yan’uwa da an jikkata wasu.

‘Yan sanda sun ce an kwantar da kura yanzu kuma komai ya lafa.

Sokoto – Rikici ya barke tsakanin ‘yan uwa mabiya akidar Shi’a da jami’an hukumar yan sanda a cibiyar daular Usmaniyya yayin Muzaharar ranar Ashura da akayi ranar Alhamis.

BBC ta ruwaito yan Shi’an da cewa yan sanda ne suka bude musu wuta lokacin da suke muzaharar.

A cewarsu, sun kammala zagayensu kenan yan sanda suka biyosu a baya suka harba musu barkonon tsohuwa.

Sun kara da cewa wannan harbi yayi sanadiyyar mutuwan akalla mutum biyu yayinda da dama sun jikkata.

Daya daga cikin ya Shi’an, Sidi Mannir Mainasara, ya laburta cewa:

“An zo wurin shafa addu’a ana jawabin kammala yan sanda sun biyomu baya sun yi harbin kan mai uwa da wabi.”

“Mutum 15 sun rigamu gidan gaskiya, sannan 13 da mumunan raunuka, daga ciki akwai karaya.”

‘Yan sanda sun karyata maganar yan Shi’a

A cewar rahoton, hukumar yan sanda ta musanta wannan magana.

Hukumar ‘yan sanda a jahar Sokoto tace da mutane unguwan Mabera ‘yan Shi’a suka fara samun matsala kuma hakan yayi sanadin barkewar rikici.

Hakan ya sa suka kai dauki domin kwantar da kuran.

Kakakin yan sanda, ASP Sunusi Abubakar

“Yan sanda sun hanzarta lokacin da bayani ya riskesu an je kuma an yi kokarin ganin cewa wani abu bai faru ba inda akayi amfani da tiya gas aka koresu aka hana wannan tashin hankalin dake kokarin ya faru.”

“Tiya gas kawai akayi amfani da shi wannan yana daidai da dokar yan sanda wajen kwantar da tarzoma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here