Rikici ya Kaure a Zauren Majalisar Ghana

Rikici ya barke a zauren majalisar kasar Ghana tsakanin yan jam’iyyar NPP da NDC.

‘Yan majalisar sun kacame da dambe kan jayayyar jam’iyyar da ke da rinjaye.

Daga bisani an tura jami’an sojoji zuwa zauren majalisar don tabbatar da doka da oda.

Rikici ya kaure a zauren majalisar Jahar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam’iyyar NPP da NDC kan wacce jam’iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri’a da ke zauren majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar NPP ce ke da rinjaye da kujeru 137 yayin da NDC ita kuma ke da kujeru 136.

Daga bisani dai an turo jami’an sojoji zuwa zauran majalisar domin dawo da doka da oda a zauren majalisar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here