Rikici ya Kunno Kai a Kungiyar Kwankwasiyya ta Jahar Kano

Rikicin cikin gida ya kaure a Kwankwasiyya ta jahar Kano bayan an zargi wani mabiyin tafiyar da yunkurin son fitowa takarar gwamna.

Kamar yadda hadimin Kwankwaso, Sanusi Surajo yayi magana, ya ce Abba Gida Gida ya samu karbuwa kuma shi zai sake fitowa, ba zasu karba kowa ba.

Tsohon Kwamishina kuma shugaban ma’aikatan fadar Kwankwaso yayin mulkinsa, Dangwani, shine ya raba kayan azumi, lamarin da yasa ya fara tara magoya baya Hargitsin cikin gida ya fara tsakanin mabiyan kungiyar Kwankwasiyya dake jahar Kano.

Hakan ta faru ne sakamakon rabon kayan abinci na azumi na miliyoyin naira da wani yayi wa ‘yan jam’iyyar a Kano.

Hadimin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanusi Surajo, ya sanar da cewa ya ga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda Dakta Adamu Dangwani ke shirin farraka kan ‘yan Kwankwasiyyan.

Dangwani tsohon kwamishinan ruwa ne kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano yayin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A zargin da ake masa, akwai na kalubalantar Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida saboda bai samu damar takara ba a 2019.

Kamar yadda Sanusi Surajo ya sanar, “Babu dan takarar gwamnan da za mu yi na’am da shi ban da Abba Gida Gida, hakan yasa zamu yi watsi da duk wani kira na daban, don haka Dangwani yayi watsi da kudirinsa ko kuma ya bar tafiyarmu.

“Hatta Kwankwaso ba zai sauya mana Abba ba, idan baka bayan Abba, toh abu mafi sauki shine ka fice da tsarin ko ka bar jam’iyyar baki daya.

“Abba ya samu karbuwa kuma ba za mu canza shi ba. Muna sane da irin zagon kasa da ake yi wa Sanata Kwankwaso kuma ba wanda zai ci galaba da izinin Allah.”

Dangwani ya fara suna ne bayan rabon kayan azumi da yayi ga ‘yan Kwankwasiyya. Yanzu haka dai yana samun magoya baya daga shugabanni da mambobin Kwankwasiyya kuma suna kira garesa da ya fito takarar Gwamnan jahar.

Har a halin yanzu, ba a ji uffan daga bangaren Dangwani ba kan zargin da ake masa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here