Ruftawar Gini: Mutane 3 Sun Mutu a Jigawa

 

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku, bayan da gini ya rufta kansu a karamar hukumar Taura da ke jihar.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce lamarin ya afku ne yau Asabar a garin Gujungu.

“Da misalin karfe 10 na safe muka samu kiran waya, inda ake faɗa mana cewa wani gini mai ya rufta. Nan da nan muka garzaya zuwa wajen, inda muka samu ginin mai hawa biyu a ƙasa,” in ji sanarwar.

Sun ce ba a kammala aikin ginin ba lokacin da ya rufta.

“Mutum uku ne suka rasa ransu nan take bayan ruftwar ginin,” in ji ƴan sandan.

An kuma samu jikkatar wasu mutum huɗu waɗanda dukkansu suka fito daga karamar hukumar Ungogo na jihar Kano, inda a yanzu ake ci gaba da yi musu jinya a asibitin Jahun.

Ƴansandan sun ƙara da cewa an ɗauki gawawwakin mutane da suka rasu zuwa asibitin.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP AT Abdullahi, ya miƙa sakon ta’azziyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu a lamarin, tare da addu’ar Allahy a gafarta musu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here