Bayan Sallamar Ministoci 5: Sababbin Ministocin da Tinubu Naɗa

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa wasu sababbi bakwai da kuma sauya wa goma ma’aikatu.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a shafinta na X, ta nuna cewa ministocin da aka cire su ne;

Waɗanda aka sallama:

1-Barr. Uju-Ken Ohanenye; ma’aikatar harkokin mata

2- Lola Ade-John; ministan harkokin yawon buɗe idanu

3- Farfesa Tahir Mamman; ministan ilimi

4- Abdullahi Muhammad Gwarzo; ƙaramin ministan gidaje da raya birane

5- Dr. Jamila Bio Ibrahim; ministar matasa

Waɗanda aka sauya wa ma’aikatu:

1-Hon Dr. Yusuf Tanko Sununu; ƙaramin ministan ilimi ya koma ƙaramin ministan jinƙai da rage talauci

2- Dr. Morufu Olatunji Alausa; ƙaramin ministan lafiya, ya koma ministan ilimi

3- Barr. Bello Muhammad Goronyo, ƙaramin ministan ruwa da tsafta, ya zama ƙaramin ministan ayyuka

4-Hon. Abubakar Eshiokpekha Momoh, ministan raya Naija Delta, ya koma ma’aikatar raya yankuna (sabuwa)

5- Uba Maigari Ahmadu, ƙaramin ministan ƙarafa ya koma ƙaramin ministan raya yankuna

6- Dr. Doris Uzoka-Anite, ministar masana’antu da kasuwanci da zuba jari ta koma ƙaramar ministar kuɗi

7- Sen. John Owan Enoh, ministan raya wasanni ya koma ƙaramin ministan kasuwanci da zuba jari (masana’antu)

8- Imaan Sulaiman-Ibrahim, ƙaramar ministar harkokin ‘yansanda ta koma ministar mata

9- Ayodele Olawande, ƙaramin ministan matasa ya koma ministan raya matasa

10-. Dr. Salako Iziaq Adekunle Adeboye, ƙaramin ministan muhalli, ya koma ƙaramin ministan lafiya

Sababbin ministocin da aka naɗa;

Dr Nentawe Yilwatda – Ministan ma’aikatar jinƙai da yaye talauci

Muhamamd Maigari Dingyaɗi – Minsitan ƙwadago

Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu – Ƙaramar ministar harkokin waje

Dr Jumoke Oduwale – Ministar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari

Idi Mukhtar Maiha – Ma’aikatar kusa da dabbobi

Hon Yusuf Abdullahi Ata – Ƙaramin ministan gidaje da raya birane

Suwaiba Said Ahmad phD – Ministar Ilimi

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here