An Nada Usman Alkali Baba a Matsayin Sabon Sifeto Janar na ‘Yan Sanda

 

IGP Usman Alkali Baba ya kama aiki gadan-gadan a matsayin sabon shugaban ‘yan sandan Najeriya.

Cire tsohon IGP, Mohammed Adamu, ya zo wa yawancin ‘yan Najeriya a bazata.

Adamu yana da kimanin wata daya da yayi masa saura na karin wa’adin shugabancinsa lokacin da aka cire shi Sifeto janar na ‘yan sanda mai barin gado (IGP), Mohammed Adamu, ya mika shugabanci ga sabon IGP mai rikon kwarya, Usman Alkali Baba.

A cewar jaridar PM News, an gudanar da bikin mika shugabancin ne a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Laraba, 7 ga Afrilu.

Jaridar The Nation wacce ita ma ta ruwaito rahoton ta bayyana cewa Adamu ya mika mulki bayan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yiwa Baba ado da sabon mukamin sa a Fadar Gwamnati, Abuja.

Da farko Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yiwa sabon Sifeto Janar na yan sanda kwalliya da karin girma zuwa IGP.

Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin sabon shugaban yan sanda.

Wadanda ke hallare a bikin kwalliyar sun hada da IGP mai barin gado, Mohammed Adamu; Sakataren gwamnati, Boss Mustapha; da Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi.

Sauran sune Malam Garba Shehu; Laolu Akande; Sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da sakataren ma’aikatar yan sanda.

Mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya.

Ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare.

Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya, maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here