Sabon Sunan da Jam’iyyar APC ta Saka wa Jam’iyyar Adawa
Fadar shugaban kasa ta radawa jam’iyyar PDP sabon sunan zolaya.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana PDP a matsayin jami’ar karya.
Garba Shehu ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta fadi zaben 2015 saboda cin hanci.
A ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu, ne fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam’iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.
A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami’ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
A cewar fafa shugaban kasa, jam’iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.
Read Also:
Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta bayar da kwangilolin bogi, na karya, domin kawai a wawure kudaden jama’a, lamarin da a karshe ya kassara tattalin arzikin kasa.
Garba Shehu ya bayyana cewa ‘yan Nigeria zasu sake juyawa PDP baya yayin zaben shekarar 2023 saboda sun gano cewa jam’iyyar babu abinda ta kunsa sai karya.
Wani bangare na jawabin ya bayyana cewa; “cin hanci ne ya jawowa jam’iyyar PDP faduwa zabe a shekarar 2015.
“Ita kuwa gwamnatin APC a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta tsare kima mutuncinta. Ta samu nasarar murkushe cin hanci a fadar shugaban kasa.
“A yanzu babu Mai kiran gwamnan banban bankin kasa (CBN) daga fadar shugaban kasa domin bashi umarnin ya kawo madarar kudi a takardun Naira, Dollar, Pounds, Euro, ko Renminbi”.
Jawabin ya bayyana cewa tasirin jam’iyyar PDP ya kare, mutuncinta tuni ya zube, Kuma ‘yan Nigeria ba zasu manta da irin ta’asara da suka tafka ba yayin mulkinsu.