An Samu Shigowar Sabuwar Cuta Mai Kashe Jama’a
‘Yan Majalisar Kogi sun ce an yi wata cuta da ke kashe Jama’a a Olamaboro.
Kawo yanzu ba a san daga ina cutar nan ta fito, ko a iya gano maganinta ba.
‘Dan Majalisar Olamaboro ya bukaci gwamnati ta kawo karshen annobar nan.
Majalisar dokokin jihar Kogi ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha su yi bincike game da sabuwar cutar da ta shigo gari a ‘yan kwanakin nan.
Bakuwar cutar da ba a kai ga gane lamarinta ba ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 50 a garin Olamaboro, Kogi.
Vanguard ta ce ‘yan majalisar jihar sun yi wannan kira ne yayin da su ka zauna a zaurensu da ke garin Lokoja a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.
Read Also:
Honarabul Anthony Ujah mai wakiltar mazabar Olamaboro a majalisar jihar ya fara kawo kukansa, ya ce cutar ta kai ga hallaka mutane har 50.
Anthony Ujah ya ce alamomin wannan muguwar cuta sun hada da ciwon kai, rikidewar idanu su yi ja-wur, gaza cin abinci da kuma wahalar yin bayan gida.
Wadanda su ka kamu da cutar nan su na fuskantar barazana wajen yin bawali da bayan gida.
Ujah ya ce mutanen kauyen Etteh da ke karkashin mazabarsa sun shiga cikin wani halin ban tausayi a sakamakon wannan cuta da ke hallaka matasa.
Dan majalisar ya ce har yanzu ba a san abin da ya ke jawo ciwon ba. Abin takaicin shi ne duk wasu magungunan gargajiya sun gagara aiki a kan cutar.
Likitoci su na aika wadanda su ka kamu da cutar zuwa dakunan shan magani da asibitoci da ke makwabta a yankunan Oguru da Okpo, amma duk a banza.
Kakakin majalisar, Prince Kolawole ya saurari batun, har ya sa aka yi tsit domin a tuna da wadanda cutar ta kashe daga watan Satumba zuwa yau.