Bayan Shekaru 7 a Kurkuku: An Saki Matar da ta Kashe Mijinta a Kano

 

Bayan shekaru bakwai da tsareta, an yafewa Rahama Hussaini da ta kashe mijinta.

Gwamnati ta saketa ne bisa shawarar da kwamitin rage cinkoso cikin gidajen yari ta bada.

Rahma ta kashe mijinta tana yar shekara 16 bayan kasa da mako guda da aure.

Kano – Kwamitin gyara da rage yawan mutane a gidajen yari ta saki Rahma Husseini, budurwar da kotu ta kama da laifin kashe mijinta a jahar Kano shekaru bakwai da suka gabata.

Kwamitin karkashin jagorancin Alkali Ishaq Bello, ta taimaka wajen sakin wasu fursunoni 30 daga gidajen yari daban-daban a ranar Juma’a, rahoton DailyNigerian.

Zaku tuna cewa a 2014, an damke Rahma Hussein, da laifin kashe mijinta rana daya bayan daurin aurensu.

Alkali R.A Sadik a 2018 ya bada umurnin jefa ta kurkuku amma zuwa lokacin da gwamnan jahar yaga dama saboda an yi mata auren dole ne kuma an yi mata aure tana yar shekara 16.

Tun daga lokacin, babu gwamnan da ya waiwayi lamarin sai yanzu da kwamitin ta kai ziyara gidajen yari don rage yawan fursunoni.

Kakakin gidajen yarin Kano, Musbahu Kofar-Nassarawa, yace an saketa ne bisa shawarar jami’an gidan yarin saboda tana da halayya na kwarai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here