Ɗan Wasan Kwallon Kafa, Saliba ya Tsawaita Zamansa a Arsenal

 

Mai tsaron baya na ƙungiyar Arsenal, William Saliba ya sanya hannu kan wani sabon kwantaragi na shekaru huɗu da ƙungiyar, wanda zai kai shi shekara ta 2027.

Ɗan wasan, ɗan asalin Faransa mai shekara 22 na daga cikin waɗanda ƙungiyar ke ji da su bayan rawar da ya taka a kakar da ta gabata.

Ya buga wasa 33 sannan ya zura ƙwallo uku.

Arsenal dai ta share tsawon kakar da ta gabata a saman teburin firimiya inda daga baya Manchester City ta kaɓo ta, sannan ta lashe kofin.

Mai horas da Arsenal, Mikel Arteta ya ce: “Ɗaya daga cikin abin da muke ta son gani shi ne Saliba ya tsawaita zamansa da mu. A kakar da ta gabata, William ya nuna mana cewa shi ƙwararren ɗan wasa ne.”

A baya an ruwaito cewa ƙungiyoyin Real Madrid da PSG sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here