Shugabar Kasar Tanzaniya, Samia ta Magantu Kan Masu Ganin Cewa Mace Bazata Iya Shugabanci ba
Shugabar kasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan ta yi magana kan yadda mutane ke hangen karfin mata wajen jagoranci a duniya.
Afirka tana kan gaba da kyawawan misalai duba ga adadin shuwagabanni mata da nahiyar ke da shi.
Shugaban kasar ta bayyana cewa hanya mafi kyau na rufe bakin masu kokwanto shine ta hanyar aiwatar da kyawawan shirye-shirye da zasu inganta rayuwar mutane da yawa.
Shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta ce ba ta taba tunanin zama shugabar kasa ba, ta kara da cewa wasu mutane ba su yarda mata za su iya shugabanci a kasarta ba.
A wata hira da BBC, Shugaba Samia ta ce lokacin da suka kira ta a shekarar 2020 don zama shugabar kasa, ta gaya musu cewa ba ta da sha’awar hakan.
Akan wahalar mulki, matar ta bayyana cewa idan aka tsara gwamnati yadda ya kamata, jaoranci na da sauƙi.
Ta ce:
“Ina kokarin gina gwamnatin hadaka domin ta yi aiki cikin nasara da kuma ci gaban kasar.”
Read Also:
Ta bayyana cewa ba wai a Afrika kawai bane aka yarda cewa mata ba za su iya mulki ba yayin da tayi tsokaci kan takaddamar da ta dabaibaye Hilary Clinton da ke fafatawa da Donald Trump shekaru da yawa da suka gabata.
Shugaba Samia ta ce ta yi matukar farin ciki cewa Afirka ta bude hanya kasancewar suna da shugabanni mata a wasu ƙasashe kamar Laberiya da Tanzania.
Ta kara da cewa:
“Ee akwai mutanen da ba su yarda mata za su iya zama shugabanni masu nagarta ba, kuma mun zo nan don nuna musu.”
Ta ce hanya mafi kyau don tabbatar wa waɗanda ba sa kimanta shugabanni mata da kyau ita ce aiwatar da kyawawan tsare -tsare da za su amfani jama’a.
Ga wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:
dr.ositaa.onyekwere ya ce:
“Ina taya Shugabar kasa murna! Na so hirar. Ki yi kyakkyawan aiki ga jama’a kuma abin da kika bari zai yi magana da kansa.”
truthbereal ya ce:
“Kai, zan iya zama kawai in saurari maganar ta!”
antonia_keza ta ce:
“Wannan matar tana da kirki sosai kuma tana da fasaha, shine karo na farko da na ji tana magana kuma zan iya cewa ta burge ni sosai.”