An Samu Gawar Shugaban APC Din da Akai Garkuwa da Shi

An tsinci gawar shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa.

Wata majiya ta kusa da iyalansu, ta shaida wa manema labarai hakan a ranar Lahadi.

Duk da dai har yanzu jam’iyyar APC bata riga ta ce komai ba a kan lamarin.

An tsinci gawar shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, bayan an yi garkuwa da shi.

Wata majiya da take kusa da iyalan mutumin ne ta sanar da jaridar PREMIUM TIMES a ranar Lahadi da rana.

Sannan wani shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya tabbatar da mutuwar Duk da dai har yanzu jam’iyyar APC ba ta riga ta yi magana ba a kan garkuwa da shi da aka yi ba.

Shugaban karamar hukumar Karu, Samuel Akala, ya tabbatar da mutuwar a shafinsa na sada zumuntar zamani ta Facebook.

Dama PREMIUM TIMES ta sanar da garkuwa da Shekwa da aka yi a ranar Asabar a gidansa da yake Lafia.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa, Dele Longe, ya tabbatar da garkuwa da shi da aka yi da safiyar Lahadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here