ALLAH ya yi wa Tsohon Sanata Sa’idu Kumo Rasuwa

 

Cike da alhini tare da tashin hankali yau Lahadi aka tashi da labarin rasuwar Sa’idu Kumo.

Tsohon sanatan kuma mai sarautar garkuwan Gombe ya rasu a asibitin Gwagwalada a Abuja.

Ya taba wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 zuwa 2003.

Allah ya yi wa tsohon sanatan Najeriya kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Gombe, Sa’idu Kumo rasuwa.

Kumo ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 71 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita, dan shi Abubakar ya sanar da Premium Times.

Ya rasu a ranar Lahadi a asibitin Gwagwalada da ke Abuja inda ya sha jinya a kan cutar da ba a bayyana ba.

Kumo ya wakilci jihar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003 a karkashin jam’iyyar APP wacce daga baya ta koma ANPP.

Ya yi mai bada shawara na musamman ga marigayi tsohon shugaban kasan Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua a 2008.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here