Sanata Ifeanyi Ubah ya Rasu

 

Ɗan majalisar dattawan Najeriya mai wakilitar Anambra da Kudu Ifeanyi Uba ya rasu.

Cikin wata sanarwar da mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon. Benjamin Kalu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya kaɗu da mutuwar Sanatan.

Rahotonni sun ce marigayin ya rasu ne a Birtaniya kwana biyu bayan wata tafiya da ya yi zuwa ƙasar domin a duba lafiyarsa.

A shekarar da ta gabata ne Sanata Ifeanyi Ubah ya fice daga jam’iyyarsa ta YPP zuwa APC mai mulkin ƙasar.

Mutuwar ɗan majalisar na zuwa ne kwana biyu bayan rasuwar shugaban ƙungiyar kare muradun ‘yan ƙabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, Chief Emmanuel Iwuanyanwu.

Tuni shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigarin da kuma gwamnatin jihar Anambra kan rasuwar sanatan da ya bayyana a matsayin ”jajirtacce”.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here