Gwamna El-Rufai Ya Siffanta Muhammadu Sanusi II a Matsayin Abokin da Kowa ya Kamata ya Samu

 

Gwamnan jahar Kaduna, ya tuna da yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

A cewarsa, abota kamar tasa da ta Muhammadu Sanusi II, ya kamata kowa ya samu irinta a duniya.

Ya bayyana sarkin a matsayin mutum masanin abin da yake aikatawa kuma mutum mai hangen nesa.

Kaduna – Gwamna Nasir El-Rufai na jahar Kaduna ya jinjinawa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda ya bayyana shi a matsayin babban abokin da kowa ya kamata ya samu, DailyTrust ta ruwaito.

Da yake magana a taron maulidin shekara-shekara na Muhammadu Sanusi II a Kaduna, El-Rufai, wanda ya yi magana ta yanar gizo kasancewar yana kasar waje, ya ba da labarin yadda su biyun suka hadu a matsayin dalibai a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Ya ce a wancan lokacin, tsohon sarkin Kano ya fito fili wajen fadin ra’ayoyinsa kuma ya bayyana hangoronsa da burinsa.

A cewarsa:

“Ya kasance mai fara’a ta zamani da ci gaba tare da tunani mai kyau wanda ya bayyana a cikin zubin yadda ya bayyana kansa.

“Wadannan halayen sun kasance tare da shi a cikin shekarun da suka gabata, yana da karfin hali kuma yana tunani cikin aiki, an san shi a matsayin daya daga cikin mafi kyawun wannan kasar da ta samar.”

Gwamnan ya ci gaba da cewa, tsawon shekarun da suka yi na abokantaka suna nuna kauna ga junansu da kuma sadaukar da kai ga kuma bayyana gaskiya ga juna.

Ya bayyana Sanusi a matsayin wanda ya yi fice a matsayinsa na malami, ma’aikacin banki kuma mai gudanarwa duk rintsi daidai gwargwado a lokacin da ya kai shekaru 40, ya kara da cewa:

“Daga nan ya ci gaba da zama Babban Ma’aikacin Banki mai daraja ta duniya, sarki mai kawo sauyi kuma fitaccen malamin addinin Islama.

“A matsayinsa na masani kan ayyukan jama’a, ya kebanta da tunani mai kyau don ci gaban Najeriya, hangen nesa na zabin tattalin arziki da wayewa wajen jagoranci na jama’a.”

Cikin dariya, gwamnan ya bayyana yadda Sanusi II ke yawan magana kan yadda shi (El-Rufai) ke sa shi ya zama kamar matsakaici.

Gwamnan ya gode masa saboda abokantakarsu da hidimar da yake yi wa Najeriya gami da Al’ummar Musulmi a matsayin babban jigo kuma Khalifa na darikar Tijjaniyya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here