Daga Yanzu ka da a ƙara Ganin Mutum Sanye da Kayan ɗan Sanda a Fina-Finai – IG Usman Baba
Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya ya gargadi masu shirya fina-finai a kasar da su guji aibanta aikin dan sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ba tare da izinin rundunar ba.
IG Usman Baba ya kara da cewa daga yanzu ka da a ƙara ganin wani mutum sanye da kayan ɗan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.
Read Also:
Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.
Masu shirya fina-finai a Najeriya kan kwaikwayi jami’an yan sandan kasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.
Sanarwar da rundunar yan sandan ta fitar ta ce “ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ƴan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan sanda.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al’umma.