Sarkin Musulmai ya Umarci Al-Ummar Musulmai da Su Fara Duba Watan Ramadana Daga Yau

 

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al’ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadana daga ranar Litinin.

Sarkin ya bada wannan umarnin ne ta hanyar shugaban kwamitin bada shawara kan al’amuran addinin musulci na fadarsa dake Sokoto.

Daga ƙarshe shugaban kwamitin fadar sarkin ya bada lambobin waya da za’a iya kai rahoton ganin watan kai tsaye zuwa ga fadar Sarkin.

Sarkin musulmi dake jahar Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar musulman ƙasar nan da su fara neman jinjirin watan Ramadana na shekarar 1442AH daga ranar Litinin.

Sarkin Musulmin ya bada wannan umarnin ne yau Lahadi a wani saƙo da shugaban kwamitin shawara kan al’amuran addinin Musulunci, Sambo Junaidu, ya fitar.

Shugaban kwamitin ya bayyana saƙon Sarkin kamar haka: “Wannan sanarwar na umurtar ɗaukacin al’ummar musulmi cewa ranar litinin,12 ga watan Afrilu, 2021 wanda ya zo dai-dai da 29 ga watan Sha’ban, 1442AH, ita ce ranar da za’a fara neman jinjirin watan Rahamadana na shekarar 1442AH.”

“Sabida haka ana umurtar musulmi da su fara neman jinjirin watan daga ranar Litinin kuma sukai rahoto idan sun ganshi.” “Ana umartar duk wnda ya ga watan da ya kai rahotonsa ga shugaban ƙauyensu don isar da saƙon ga fadar mai martaba Sarkin Musulmi”

Sarkin ya kuma yi addu’ar Allah ya taimaki musulmai gaba ɗaya wajen sauke nauyin da ya ɗora musu na yin azumin wata ɗaya (Ramadan). Malam Junaidu ya kuma bada lambobin wayan da za’a kai rahoton ganin jinjirin watan kai tsaye zuwa ga kwamitiin kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Lambobin wayan sun haɗa da: 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322 da kuma 08035945903.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here