Zazzau: Sabon Sarkin Zai Jagoranci Kwamitin Matasa da Kungiyoyar NGF

An nada Kwamitoci bayan taron da Gwamnonin Arewa su ka yi a Kaduna.

Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ne aka zabi ya rike kwamitin Matasa – Kusan wannan ne aikin farko da Sarkin zai yi tun bayan hawa gadon mulki A ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2020, gwamnonin Arewa da manyan gwamnatin tarayya su ka yi wani muhimmin taro a jihar Kaduna.

Legit.ng ta samu labarin matsayar da aka cinma bayan wannan zama, daga ciki za ayi amfani da Sarakunan yankin wajen kawo zaman lafiya. Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli da takwaransa na kasar Lafia, Sidi Bage Muhammad su na cikin wadanda aka zaba su rike kwamitocin.

Kungiyar NGF ta zabi Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya shugabanci kwamitin da zai yi aiki da matasa da duk kungoyoyi masu zaman kansu.

‘Yan wannan kwamiti za su hada da wakili guda daga kowane yanki na kasar, da kuma wakilan matasa da nakasassu daga jihohin yankin Arewa.

Bayan haka mata da ‘yanmata za su samu wakili guda daga kowace shiyya. Kwamitin zai samu wakilcin malaman kiristoci da musulunci. Ragowar ‘yan kwamitin su ne ‘yan kasuwa da kuma wakilin sufeta janar na ‘yan sanda.

Kamar yadda kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ta bada umarni, wannan kwamiti da takwarorinsa za su fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnonin sun yaba da kokarin da sarakunan gargajiya su ke yi wajen kawo zaman lafiya ganin abin da ya faru wajen zanga-zangar #EndSARS.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here