Satar Mazakuta: Fusatattun Matasa Sun Farma ‘Dan Achaba a Abuja

 

Wani abun bakin ciki ya afku a yankin Nyanya da ke Abuja bayan fusatattun matasa sun far ma wani dan achaba mai suna Yahuza har lahira.

An rahoto cewa wasu fusatattun matasa sun farmaki marigayin bayan fasinjarsa ya koka cewa bai ga mazakutarsa ba.

An tattaro cewa jami’an tsaro sun isa wajen bayan an dauki dan keken zuwa asibiti inda ya mutu.

Abuja, Nyanya – Wasu fusatattun matasa sun farmaki wani dan achaba mai suna Yahusa, kan zargin sace mazakutar fasinjansa a yankin Nyanya da ke Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wani ganau mai suna Ibrahim Musa, ya ce mummunan al’amarin ya afku ne da misalin karfe 5:12 na yammacin ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba

Musa ya yi bayanin cewa dan acahaban ya dauki fasinja daga ‘Old Karu’ zuwa Nyanya amma jim kadan bayan fasinjan ya sauka daga achaban sai ya koka cewa bai ga mazakutarsa ba.

Wani ganau ya ce kokawar da ya yi ya ja hankalin wasu mutane, wadanda suka far ma dan achaban da sanduna da muggan makamai.

Ya kara da cewar daga bisani wasu masu wucewa sun ceci dan achaban sannan suka dauke shi zuwa asibiti mafi kusa.

Musa ya ci gaba da cewa an dauki dauki shima fasinjan zuwa wani asibiti a Nyanya don tabbatar da ikirarinsa na rasa mazakutarsa.

“Abun takaici, dan achaban ya rasu daga bisani a asibitin da aka kai shi kafin jami’an tsaro su isa wajen.”

Ihun batan mazakuta duk karya ce Kakakin yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ya ce dukkan batutuwan batan mazakuta duk karya ce.

Adeh ta bayyana cewa an kai mutane da dama kotu kan irin wadannan zarge-zargen.

Kakakin yan sandan ta ce:

“Kwamishinan yan sandan ya bukaci mazauna yankin da su gaggauta kai rahoton irin wannan lamarin ofishin yan sanda domin laifi ne daukar doka a hannu; wadanda aka kama da hannu a lamarin za su fuskanci mataki na doka.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com