An Sauke Shugaban ƙaramar Hukumar Kumbotso Dake Jihar Kano

 

Wata babbar kotu a jihar Kano ta soke nasarar Abdullahi Ghali Shitu a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, tare da umartar a bi hukuncinta na baya da ya ayyana Ali Musa Dan Maliki a matsayin halastaccen wanda ya lashe takarar.

Kotun ta jaddada cewa hukuncin da ta yanke tun ranar 25 ga watan Oktoban 2024 yana nan daram, inda ta ce Ali Musa Dan Maliki shi ne ya cancanci riƙe mukamin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso bisa tanadin doka.

Bangaren Ali Musa Dan Maliki ne suka garzaya kotu bayan da gwamnan jihar, Abba kabir Yusuf ya rantsar da Abdullahi Ghali Shitu ranar 14 ga watan Nuwambar 2024 a matsayin shugaban karamar hukumar

Da wannan hukuncin, kotun ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da hukuncin ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da bin doka da oda a harkokin mulki a matakin ƙaramar hukuma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here