Sauyawa Najeriya Suna: Shahararren Mawaki, Naira Marley ya Bayyana Cewa Zai Rera Sabuwar Wakar Taken Hadaddayar Jamhuriyar Afrika

 

Shahararren mawaki Naira Marley ya bayyana aniyarsa ta rera sabuwar wakan take ga sabuwar kasa.

Ana ta cece-kuce bayan tura kudurin sauyawa Najeriya suna zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar Afrika (UAR).

A nasa gudunmawa, Naira Marley ya ce zai dauki babban aikin rera wa kasa take idan magana ta tabbata.

Shahararren mawaki, Naira Marley ya bayyana cewa zai yi zaman jira don rera sabuwar wakar taken kasa bayan yanke shawarar sauya sunan Najeriya zuwa Hadaddiyyar Jamhuriyar Afirka (UAR).

A cewar rahotanni, Adeleye Jokotoye, kwararre kan haraji, ya gabatar da shawarar ga kwamitin a taron sauraron kararrakin yankin Kudu maso Yamma da ke Legas a ranar Laraba, 2 ga Yuni, 2021, jaridar Pulse ta ruwaito.

Yayin da yake gabatar da wannan shawara, ya ce sunan Najeriya turawan mulkin mallaka ne suka tilastawa kasar kuma ya kamata a canza shi.

A nashi bangaren na gudunmawa, Naira Marley ya bayyana a shafinsa na Twitter don bayar da gudunmawarsa kyauta ga sabuwar kasar, UAR.

A cewarsa, ya yarda ya dauki matsayin Pa Benedict Odise wanda ya rera wakar taken Najeriya ta biyu a shekarar 1978. Ya rubuta a Twitter: “Omo Ni ne zan rera sabuwar wakar taken UAR.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here