Secondus ba Zai Iya Doke APC a Zabe Mai Zuwa ba – Gwamna Wike
Nyesom Wike yana ganin PDP tana bukatar sauyin shugabanci kafin 2023.
Wike yace Prince Uche Secondus ba zai iya doke APC a zabe mai zuwa ba.
Wannan ya sa Gwamnan na Ribas ya dage sai an canza shugabannin PDP.
Gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, yace shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus da ‘yan majalisarsa, ba za su iya kai su ga nasara a 2023 ba.
Jaridar The Nation ta rahoto Nyesom Wike yana cewa ganin gazawar Prince Uche Secondus ya sa ya dage a kan sai an canza shugabannin jam’iyyar PDP.
Mai girma gwamnan ya hakikance a kan cewa raunin majalisar aiwatarwa ta NWC ya jawo aka samu sabani tsakanin ‘ya ‘yan babban jam’iyyar adawar.
Read Also:
Da yake magana da manema labarai a Fatakwal a ranar Talata, Nyesom Wike yace jam’iyyar PDP ce kadai za ta iya karbe mulki a hannun APC a kasar nan.
“Idan ka shiga cikin jama’a ka tambaye ‘yan Najeriya ko PDP ta shirya karbar mulki a 2023, idan aka yi kuri’a, za ka gane cewa mutane suna ma jiran PDP ne.”
“Tsoron da ‘yan Najeriya suke yi shi ne ko PDP ta shirya karbe mulki. Saboda haka, dole mutane suka damu a kan haka. PDP sai ta nuna za ta hau mulki.”
“Kuma muka ce idan aka tafi a yadda ake a yau, zai yi wahala a karbi mulki a 2023, sai an yi gyara.”
Wike yace a karkashin Prince Secondus, akwai raunin shugabanci, ‘yan majalisar NWC da suke ofis a yau, ba za su iya kai jam’iyyar ga dawo wa mulki ba.
“Babu mai cewa sun yi kokari ko ba su yi ba, muna maganar kalubalen da yake gaba ne. Shiyasa mu ke so jam’iyya ta samu wadanda za su iya jagorantar ta”
Gwamnan yake cewa duk wanda ya san APC, ya san cewa ana bukatar ayi da gaske, sai PDP ta jajirce domin ta tunkare ta, har ta iya karbe mulki daga hannunta.