Sergio Ramos Zai Bar Real Madrid

 

A jiya ne kwantiragin Sergio Ramos ya kare da kungiyar Real Madrid.

Real Madrid da ‘dan wasan ba su amince a kan sabunta kwangilarsa ba.

Tauraron bayan zai tashi daga kungiyar da ya yi shekara 16 yana wasa.

Sanarwar ban kwana da club

Kungiyar Real Madrid ta bada sanarwar cewa Sergio Ramos zai tashi daga club din. Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni, 2021.

Ga abin da sanarwar da ta fito daga shafin yanar gizon kungiyar take cewa:

“Za a kira taron manema labarai a ranar Alhamis, inda za a sanar da tashin kyaftin din Real Madrid bayan shekaru 16.”

“Shugaban club, Florentino Perez, zai bayyana tare da ‘dan wasan da ya lashe gasar cin kofin Duniya da kasar Sifen.”

Sergio Ramos zai bayyana ta kafar yanar gizo.

Za ayi zaman ne da karfe 12:30 na rana.

Tarihin Sergio Ramos a Madrid

Marca ta ce Sergio Ramos ya zo Madrid ne daga Sevilla a 2005, ya samu damar buga wasanni 671.

Bayan ya dade a kungiyar, ya zama mai rike kambun ‘yan wasa.

Daga cikin kofin da ‘dan wasan ya ci har da kungiyar Real Madrid akwai La Liga biyar, Copa del Reys biyu, gasar cin kofin Turai biyu da kofin kulob na Duniya hudu.

A lokacin da yake bugawa Real Madrid ne Ramos ya ci gasar Euro har sau biyu a kasar Sifen. Haka zalika tauraron ya ci kofin kwallon Duniya a shekarar 2010.

Bayan zamansa kyaftin, Ramos mai shekara 35 ya na da kwallaye fiye da 100. Ba kasafai ne aka saba ganin ‘dan wasan baya mai irin wadannan tulin kwallaye ba.

A shekarar bana, Ramos bai buga wasanni da dama ba saboda rashin lafiya. Hakan ya jawo har ya gagara zuwa gasar cin kofin Turai wanda ake yi a kasar Hungary.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here