Lauyan da ke Jarogantar Shari’ar Zakzaky da Matarsa ya Nemi Kotu da ta Yanke Musu Hukunci

 

Lauyan da ke jarogarantar shari’ar Zakzaky da matarsa ya nemi kotu da ta sallami karar ta yanke hukunci.

Lauyan yayi bayyana haka ne ga manema labarai biyo bayan dage karar da alkali yayi zuwa 25 ga watan Mayu Lauyan ya roki kotun da ta duba yiyuwar yankewa Zakzaky da matarsa hukuncin da doka ta tanada Dari Bayero, babban lauyan da ke jagorantar ‘shari’ar sirri’ na jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN), Sheikh Ibrahim Zakzaky, da matarsa Zeenat, ya roki Babbar Kotu da ta dakatar da tuhumar ta yanke masu hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Bayero, yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan Mai Shari’a Gideon Kurada ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Mayu domin wadanda ake tuhumar su bude kariya kan karar, ya ce jahar ta rufe kararta bayan gabatar da shaidarta ta 15 a shari’ar.

“Daya daga cikin addu’o’inmu shi ne kotu ta yanke hukunci a kan Babu-Shari’ar-Gabatarwa, ta yi watsi da masu kariyar kuma ta hukunta wadanda ake tuhumar yadda ya dace da kuma yanke musu hukunci kamar yadda doka ta tanada,” inji shi.

Amma lauyan Shaikh Zakzaky, Femi Falana (SAN), ya fadawa manema labarai cewa tawagarsa za ta bude bada kariya a kan karar a ranar da aka dage, Daily Trust ta ruwaito.

Falana, wanda Marshall Abubakar ya wakilta, ya ce, bayan sun yi shawara kan fayil din wadanda ake tuhuma za su shigar da neman sallamar karar a gaban kotu.

A cewarsa, tun da farko mai gabatar da kara ya roki kotu da ta dakatar da tuhumar, ya kara da cewa, “Ya zuwa yanzu kuma kamar yadda shari’ar ta nuna, shaidu 15 na masu gabatar da kara ba su kafa hujja kan wadanda ake kara ba.”

A baya dai gwamnatin Jahar Kaduna ta tuhumi El-Zakzaky da Zeenat da aikata laifuka guda takwas wadanda suka hada da kisan kai, yin taro ba bisa ka’ida ba da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, da sauran tuhume-tuhume.

Shugaban IMN din da matar sa sun musanta aikata laifukan lokacin da aka karanta masu tuhumar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here