Amurka/Iran: Sharuɗɗan da Iraq ta Gindaya Kan Kawo ƙarshen Yaƙin
Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito cewa ƙasar ta yi watsi da buƙatu da sharuɗan da Amurka ta gindaya na kawo ƙarshen yaƙin.
Tashar ta ruwaito hakan ne daga wata majiyar tsaro da ba ta bayyana ba, amma majiyar ta ƙara da cewa, “Iran za ta kawo ƙarshen yaƙin ne a lokacin da take so, ko kuma aka cika mata sharuɗan da ta gindaya.”
Hukumomi a Iran dai sun sha nanata cewa ba tsagaita wuta suke so ba, yaƙin baki ɗaya ne suke so a dakatar.
Read Also:
Haka kuma kafar ta ruwaito cewa Iran ta gindaya nata sharuɗan guda biyar kamar haka:
Dakatar da hare-hare da kashe-kashe a ƙasarta
Fitar da tsari mai kyau da zai tabbatar ba a sake ƙaddamar da yaƙi a Iran ba
Tabbatar da tsarin biyan diyya
Kawo ƙarshen yaƙi a ƙasar da sauran ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ita a yankin
Ƙasashen duniya su tabbatar da iko da ƴancin Iran wajen gudanar da mashigar Hormuz
Kafar ta ƙara da cewa Amurka na ƙoƙarin ganin an shiga tattaunawar, amma Iran na nuna cewa buƙatun na Amurka sun yi “tsauri.”






