Shawarar da Aisha Yesufu ta ba wa ‘Yan Kungiyar IPOB

 

Aisha Yesufu ta ba ‘Yan kungiyar IPOB su hada-kai da Jam’iyyar APGA a yankin Kudu maso gabas.

‘Yar gwagwarmayar tace IPOB za ta iya amfani da farin jininta, ta rika juya akalar siyasar yankin.

Yesufu ta na ganin zai fi kyau kungiyar ta shiga siyasa da kyau, ta daina tilastawa mutanen Ibo kulle.

Nigeria – Aisha Yesufu tayi kira ga kungiyar tsageru na Indigenous People of Biafra ta hada-kai da jam’iyyar hamayya ta All Progressives Grand Alliance.

Shahararriyar ‘yar gwagwarmayar ta bukaci ‘yan IPOB da jam’iyyar ta APGA su hada-kansu domin su dunkule mutanen yankin kudu maso yamma.

Aisha Yesufu tace a maimakon IPOB ta rika bata lokacinta wajen bada umarnin kowa ya zauna a gida, ya kamata ta maida hankali wajen samun kuri’u.

Punch ta rahoto Yesufu tana ba kungiyar tsagerun shawarar tayi amfani da muryar da farin jininta wajen ganin ‘yan takara masu nagarta sun ci zabe.

Wannan Baiwar Allah tayi wannan magana ne bayan ganin sakamakon zaben jahar Anambra da Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya yi nasara.

Abin da Aisha Yesufu take cewa

“Ina ma a ce kungiyar IPOB tayi aiki da jam’iyyar APGA wajen juya siyasar Kudu maso gabas?” – Aisha Yesufu.

“Su kawo ‘yan takarar da suka dace, su lashe zabe. Su nuna mana yadda mutane masu nagarta da cancanta da kwarewa za su iya kawo canji a siyasa.”

IPOB su shiga a rika damawa da su a siyasa

Jaridar kuma ta rahoto jagorar ta tafiyar BBOG tana cewa kungiyar IPOB za ta iya amfani da karfinta wajen samun yadda ta ke so a gwamnatin tarayya.

“Tarayyar APGA/IPOB za ta iya dunkule kudu maso gabas a siyasance. A maimakon IPOB ta yi ta asarar bada umarnn kulle, sai su kawo ‘yan takara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here