Garba Shehu ya Shawarci ‘Yan Jarida da su Tsarkake Ayyukansu

 

Mataimakin shugaban kasa kan yada labarai ya yaba da ci gaban da gwamnatin Ganduje ta kawo.

Ya ce duk masu kushe da suka ga gwamnatin a baya, yanzu sun cika da zunzurutun nadama.

Ya kuma shawarci ‘yan jarida da su tsarkake ayyukansu da yada labarai da zasu dinke baraka.

Garba Shehu, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wadanda suka yiwa gwamnan jahar Kano tawaye a baya yanzu haka suna cike da nadama, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake jawabi a lokacin bude taron shekara ta 2021 na kungiyar Editocin Najeriya ranar Litinin a Kano, Shehu ya ce jahar ta samu ci gaba da yawa, cika alkawura da kuma sulhu a karkashin jagorancin Ganduje.

Ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na bukatar a basu kwarin gwiwa cewa gwamnatoci a dukkan matakai na aiki kai tsaye don kawo karshen rashin tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ganin yadda labaran karya da tada hankali suka yi yawa a Najeriya, Mista Shehu ya yi kira ga editoci a wurin babban taron da su ci gaba da inganta zaman lafiya da hadin kai ta hanyar rahoton da suke bayarwa ta kafafen yada labarai, PM News ta kawo.

Ya kuma kalubalanci editocin da su yi amfani da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen dinke barakar da ke tsakanin gwamnati da jama’a, musamman ta fuskar yada labarai.

“Ina ganin lokaci ya yi da za mu sa ido mu ga yadda za mu dakatar da yada labaran karya, sakaci da jita-jita. “Ina ganin ya kamata mu ma mu yi amfani da wannan damar don tunatar da kawunanmu nauyin da ke kanmu na inganta aikin jarida,” in ji Shehu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here