Buhari: Caccakar da Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi wa ‘Yan Majalisar Wakilai

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki ‘yan majalisar wakilai.

A cewar sanatan, ‘yan majalisar suna tsoron Buhari ne shiyasa suka fasa gayyatarsa.

Ya ce ya kamata a ji ta bakin shugaban kasa musamman yadda ake yawan kai farmaki garuruwa.

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce ‘yan majalisar wakilai suna tsoron shugaba Muhammadu Buhari, shiyasa suka soke gayyatar da suka yi masa.

Sani ya yi wannan maganar ne da BBC Hausa, inda yace ya kamata shugaba Buhari ya bayyana gaban majalisar don amsa tambayoyi a kan matsalolin tsaron dake addabar Najeriya.

A cewarsa, babu dalilin da zai sanya a ce su gayyaci Buhari kuma su koma su canja ra’ayi.

“Ana ta kashe mutane a kowacce rana, ana ta garkuwa da dubbannin jama’a dare da rana kuma alamu sun nuna cewa shugaban kasa bai damu ba. Wadannan suna cikin dalilan da suka sanya aka maka Jonathan da kasa.

“Menene amfanin fasa gayyatar shugaban kasa? Hakan yana nuna kuna tsoron shi ne. A kalla gayyatar za ta sanya shugaban kasa yayi wa ‘yan Najeriya bayani su san matakan da yake kokarin dauka,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here