Shugaban Boko Haram,Abubakar Shekau ya Gargadi Sababbin Hafsoshin Tsaro

Shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da sabon sako game da sabbin manyan hafsoshin tsaro.

A sakon mai tsawon kimanin mintuna 9, Shekau ya shaidawa sabbin shugabannin sojojin cewa babu wani abu da za su iya yi da magabatansu ba su yi ba.

Bayan ambaton sunayensu da ayyukansu, Abubakar Shekau ya yi kira gare su da su tuba su rungumi musulunci.

Abubakar Shekau, shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram ya fitar da sabon sautin murya inda ya yi magana game da nadin sabbin manyan hafsoshin Najeriya, inda ya ce babu wani abu da za su iya tabukawa da magabatansu ba su yi ba a yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, HumAgle ta ruwaito.

A sautin da ya fitar mai tsawon mintuna tara da dakika 56, Shekau ya ce ya ji labarin yi wa tsofafin manyan hafsoshin tsaron murabus da maye gurbinsu da sabbi amma ya yi kira garesu su amshi musulunci.

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus tare da maye gurbinsu da sabbi.

Kungiyoy da mutane da dama sun dade suna kira da shugaban kasar ya sauya manyan hafsoshin tsaron.

A cikin sabon sautin muryar da Shekau ya fitar, ya ambaci sunayen manyan hafsohin tsaron daya bayan daya da ayyukansu sannan ya yi kira garesu da su tuba domin babu wani abu da za su iya yi domin tarwatsa kungiyarsa.

“Leo Irabor, shugaban sojoji, ka tausayawa kanka, ka tuba ka amshi musulunci. Babu abinda zaka iya yi,” in ji Shekau.

Ya ce Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya dena rudar kansa domin shi musulmi ne.

“Ko da kai musulmi ne amma kana yin shirka, yanzu kai ba musulmi bane,” in ji Shekau.

Wata majiya da ke da masaniya kan ayyukan Boko Haram ta shaidawa HumAngle cewa akwai yiwuwar kungiyar na shirya kai babban hari don ya zama ishara ga sabbin manyan hafsoshin tsaron cewa ba za su saduda ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here