Sakataren Kungiyar ‘Daliban Shi’a ya Bayyana Cewa an Kashe Musu Mutane 6 a Abuja

 

Sakataren kungiyar daliban Shi’a yace an kashe musu mutum shida.

Ya Zargi jami’an tsaron da tafiya da gawawwakin wadanda aka kashe.

Yan Shi’a sun yi muzaharar Arba’in a birnin tarayya Abuja.

Abuja – Harbe-harben bindiga akan babban titin Kubwa kusa da Gwarinpa Estate ranar Talata yayinda jami’an tsaro sukayi kicibis da mabiyar akidar Shi’a masu zanga-zanga.

Ana zargin cewa mutum shida sun hallaka yayinda wasu sun jigata.

An zargi jami’an tsaron da budewa masu zanga-zangan wuta yayinda suka muzaharar Arba’in.

Sakataren daliban Zakzaky, Abdullahi Musa, bayyanawa Sahara Reporters cewa jami’an tsaro sun yi awon gaba gawawwakin.

Yace:

“Kawai harbin mutane sukeyi. Yanzu haka da nike magana an kashe mutum shida. Kai har sun yi awon gaba da gawawwakin.”

Mambobin kungiyar shi’ar sun fito ranar Alhamis domin muzaharar cikar ranaku 40 da bikin jimamin ranar kisan Imam Husseini, jikan Manzon Allah (SAW) wanda aka kashe ranar 10 ga Muharram.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here