Amurka/Iran: A Shirye Muke mu Karɓi Baƙuncin Tattaunawar Kawo ƙarshen Yaƙin – Pakistan
Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif ya yi tayin karɓar baƙuncin tattauanwar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.
Read Also:
Cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na sada zumunta Mista Sharif ya ce idan Amurka da Iran sun amince Pakistan za ta karɓi baƙuncin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.
Haka shi ma takwaransa na Indiya Narendra Modi ya ce ”ya yi tattaunawa mai armashi da Shugaba Trump na Amurka game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
”Na yi waya da shugaban Amurka, kuma mun yi tattaunawa mai armashi kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya. Indiya na goyon bayan kawo ƙarshen yaƙin domin samun zaman lafiya”, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.






