Shugaban Alkalan Najeriya, Justice Tanko Mohammad ya yi Murabus Daga Kujerarsa

 

Shugaban Alkalan Najeriya, Justice Tanko Muhammad, ya yi murabus daga kujerarsa biyo bayan rikicin da ya barke tsakaninsa da sauran alkalan kotun kolin Najeriya.

Channels Tv ta ruwaito cewa Alkali Tanko Mohammad ya yi murabus ranar Lahadi kuma yace ya ajiye aikinsa ne sakamakon rashin lafiya.

Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana shirin nada Justice Olukayode Ariwoola, matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa za’a sanar da murabus dinsa nan ba da dadewa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here