Shugaban NITDA ya Halarci Bikin Sallah a Rana ta Biyu a Haɗejia

A cigaba da ziyarar sallah da ya ke yi a mahaifarsa, (Haɗejia, Jihar Jigawa), mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya halarci bikin hawan sallah a wannan rana ta biyu cikin shagulgulan sallar.

Hawan Sallah

Hawan sallar wanda mai martaba sarkin Haɗejia, Alhaji Dakta Adamu Abubakar Maje Haruna (CON) ya gudanar shi da hakimansa, ya samu halartar sauran manyan baƙi, inda mai martaba ya ziyarci bariki kamar yadda aka saba duk shekara bisa al’ada da aka gada tun fil’azal.

Talata, 3 ga watan Maris, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here