Shugaban Jam’iyyar PDP da Sauran Shugabannin Jam’iyyar a Jahar Ebonyi Sun Koma APC
Onyekachi Nwebonyi, shugaban jam’iyyar PDP a jahar Ebonyi ya koma APC.
Suma sauran shugabannin jam’iyyar sun dunguma sun sauya sheka zuwa APC.
Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki Shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam’iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a jahar.
Read Also:
Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam’iyyar, The Nation ta ruwaito.
Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.
Idan za a iya tunawa, shugabannin jam’iyyar PDP na kasa a karshen shekarar 2020 sun kori Nwebonyi daga jam’iyyar bayan gwamnan jahar ya koma APC.
Amma shi da sauran shugabannin jam’iyyar a jahar sun tafi kotu domin kallubalantar korarsu.
A watan Fabrairu, babban kotu da ke zamanta a Abakaliki sun soke korar da aka musu sun kuma rushe kwamitin riko ta Fred Udogu da shugabannin jam’iyyar suka naɗa. Kwamitin na Udogu ta tafi kotu domin ɗaukaka kara kan rushe ta kuma kawo yanzu kotu bata yanke hukuncin kan batun ba.